Macron-Faransa

Ina son a yi wa Afrika sassauci kan bashin da ke kanta-Macron

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron Romain Ferré/RFI

A zantawa ta musamman da RFI, shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana goyon bayansa ga shirin yi wa kasashen Afirka sassauci dangane da basusukan da  ke wuyansu. A wannan zantawa, Macron ya kuma tabo batutuwan da suka shafi yadda za a yaki annobar coronavirus da kuma yaki da ayyukan ta’addanci musamman a yankin Sahel da kuma zagayen Tafkin Chadi.

Talla

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakkiyar hirar Macron da RFI

Ina son a yi Afrika sassauci kan bashin da ke kanta-Macron

 

 

 

 

 

Ga yadda zantawar shugaba Macron ta kaya da Radio France Internationale a rubuce:

RFI : Mai girma shugaban kasa, lokacin da ka ke gabatar da jawabi ga al’ummar Faransa shekaranjiya Litinin, mun ji ka tabo batutuwan da suka shafi sauran kasashen duniya ciki har da dimbin basusukan da ke wuyan Afirka, ko wannan na nufin cewa fargabar da ka ke da ita ba wai ta takaita ne ga kasar Faransa kawai ba har ma da nahiyar Afirka ?

Emmanuel Macron :Kwarai da gaske, saboda na lura cewa halin da muke ciki a yau lamari ne da ya shafi kowacce nahiya. Muna cikin mummunan yanayi sakamakon yadda wannan annoba ta riske mu, kuma ya zama wajibi kasashe masu karfin tattalin arziki su yi wani abu akai.

Duba ka gani abin da ke faruwa hatta a kasashen da suka samu ci gaba ta fannin kiwon lafiya, kamar Amurka, Yankin Turai da kuma China..Saboda haka idan ka dubi halin da Afirka ke ciki a fannin kiwon lafiya, tattalin arziki da kuma sauyin yanayi, ya zama wajibi mu nuna wa nahiyar zumunci.

RFI : wani abu da ka ke kokarin ganin kasashen duniya su dauki mataki na bai-daya shi ne batun tattalin arziki. A kowacce shekara, kasashen Afirka na biyan bashin Dala bilyan 365 da ke wuyansu, yaya za ka tunkari kasar China, Turai, Amurka da sauransu, domin ganin sun yafe wa nahiyar Afirka wannan bashi mai tarin yawa ?

Emmanuel Macron : idan aka yi la’akari da yadda illahirin kasashen duniya suka kalli wannan annoba, za a fahinci cewa lalle sun yarda akwai matsala, ka dauka tun daga manyan bankuna a kowacce kasa, babban bankin Birtaniya, Asusun Tallafa wa Kasashe na Turai, har zuwa Babban Bankin Turai, dukanninsu a cikin watan Maris sun sanar da tsare-tsare suka dace don tunkarar wannan matsala.

Amma a nahiyar Afirka ba mu ga wani mataki makamancin wannan ba, saboda ba su da zarafin yin hakan, yayin da a dayan bangaren, wadannan kasashe ke fuskantar matsalar sulalewar makudaden kudade zuwa ketare.

Wadannan kasashe ba su da wata madafa face su tunkari asusun IMF don samun wani tallafi da zai kai Dala bilyan 500. Ya kamata mu goyi bayan wannan shiri.

A dazun, ka ambaci dimbin bashin da ke wuyan kasashen Afirka, Kowace shekara, kashi 1 cikin uku na kudaden cinikin da Afrika ke yi da kasashen ketare ana amfani da su ne domin biyan bashi, wannan abu ne mai tada hankali! Ina fatan ganin an samu sauki ga wannan matsala, saboda abu ne da bai kamata ya ci gaba da faruwa ba.

A shekaranjiya lokacin da nake gabatar da jawabi, na fito fili karara inda na bukaci a samar da wani shirin yafe wa wadannan kasshe basusukan da ke wuyansu.

Mun tattauna don cimma wannan buri a cikin gajeren lokaci, Kungiyar Tarrayar Afirka ta nada manzanni 4 na musamman kan wannan batu, kuma tuni suka gabatar da shawarwari.Shawara ta farko ita ce jinkirta wa kasashen biyan bashin da ke wuyansu, lura da cewa soke biyan bashi abu ne da ke daukar dogon lokaci.

Idan an ce, jinkirta biyan bashi, wannan na nufin cewa ba za a biya kudin ruwa a lokacin da aka tsawaita wa kasashen da ake bi wannan bashin ba. A marecen wannan Labara, gungun kasashen G20 za su bayyana matsayinsu kan wannan batu.

Muna ci gaba da aiki don ganin cewa gungun Paris Club, da China, da Rasha, da kasashen Yankin Gulf da sauran kasashe ko Cibiyoyin Bayar da Lamuni sun dauki irin wannan mataki. Wannan zai kasance karo na farko a tarihin duniya.

Yau kowa ya sani cewa muna cikin matsala, saboda haka ya kamata a bai wa kasashen Afirka damar numfasawa, kuma ba ta yadda za su numfasa face a jinkirta biyan bashi da kuma kudin ruwa da ke wuyansu. Ina jin cewa wannan zai kasance muhimmin ci gaba.

RFI :Lura da cewa kashi 40% na basusukan da ke wuyan kasashen Afirka mallakin kasar China ne, ko ka zanta da shugaba Xi Jinping dangane da wannan batu ?

Emmanuel Macron:Lalle ban yi magana da shi a game da wannan batu ba, amma na san muhimmancin Afirka a gare shi. Ba na shakkar cewa halin da ake ciki a yau, Afirka ta cancanci a yafe mata mafi yawan basusukan da ke wuyanta.

Ka bayyana cewa mafi yawan kudaden bashin da ke wuyan Afirka mallakin kasar China ne, to ba wai China kawai ba, muna fatan sauran, za su hubbasa don ganin cewa nahiyar ta mirmirje daga matsalolin da ta fada.

RFI: to mun samu labarin cewa dakarun sojin Faransa 4 da ke aiki a runduanr Barkhane sun harbu da cutar Coronavirus, kuma tuni aka dawo da uku daga cikinsu gida, ko an samu karin wasu sojojin bayan wadannan hudu?

Emmanuel Macron : Lalle akwai kalubale sakamakon wannan annoba, muna sa ido sosai don kare lafiyar dakarunmu na Barkhane. Da farko na tattauna da shugabannin kasashe 5 da suke aiki a cikinsu a yankin Sahel. Saboda haka kafin dawo da su a gida Faransa, sai da aka kebe su tsawon lokaci a kasashen da suka harbu da cutar.

A game da ayyukan soji kuwa, cikin makonnin da suka biyo bayan ganawar da muka yi a birnin Pau, ni da sauran takwarorina na kasashen yankin Sahel mun yi kokarin kafa sashen tara bayanan sirrin ta fannin tsaro da ke da babbar cibiyarsa a birnin Yamai.

Tuni muka fara samun sakamako mai karfafa guiwa, domin mun kaddamar da farmaki sau da dama a yankin Gurma da ke kan kusurwar kasashen nan uku da ke fama da ‘yan ta’adda, mun samu gagarumar nasara a wasu hare-haren da muka kai wa ‘yan ta’addar cikin kasahen Nijar da Mali.

RFI:To ko an sake samun wasu sojojin Faransa da suka kamu da wannan cuta?

Emmanuel Macron : Ba ni da wata masaniya ko an samu sabbin kamuwa, amma abu na biyu da ni ke son yi tsokaci akai shi ne, gagarumin farmaki kan mayakan Boko Haram da mataimakanta da aka kai zagayen Tafkin Chadi.

Zan yi amfani da wannan dama domin nuna alhini ga al’ummar kasar Chadi, saboda asarar da suka samu a baya-bayan nan. To sai dai zan kara jinjina wa al’ummar kasar dangane da nasarar da suka samu kan ‘yan ta’adda. Dakarun Chadi sun taka gagarumar rawa a cikin kasarsu da kuma kare kasashe makota wato Nigeria, Nijar da Kamaru.

Zan yi masu jinjina sannan in yaba wa shugaba Idris Deby, domin sun kare kasarsu da ma sauran kasahe makota daga sharrin ‘yan ta’adda.

Lalle wannan lamari ya hana wa Chadi tura bataliyar da ta dauki alkawari a taron da muka gudanar a birnin Pau, amma gaskiya na fahinci dalilan mahukuntan kasar, domin ta’addanci ba wai ya takaita ne kawai a kan kusurwar kasashen uku na yankin Sahel ba, a’a, akwai shi hatta ma a zagayen Tafkin Chadi.

RFI: Makonni biyu da suka gabata, a zantawarsa da RFI da France 24, Sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya bukaci a wannan lokaci da ake fama da annobar coronavirus a tsagaita wuta a duk inda ake yaki a duniya, wasu kungiyoyi kamar kasar Kamaru, sun karba wanna kira, Saudiyya ma ta sanar da tsagaita wuta a kasar Yemen, to amma kasashe 5 masu kujerun dindindin a Kwamitin Sulhu sun yi gum da bakunansu ?

Emmanuel Macron: Ba haka ba ne, domin kuwa Faransa ta jaddada irin wannan kira, abin da muke fata shi ne kasashen biyar kamar yadda ka fada su zauna tare da yin kira da murya daya domin samar da tsagaita wutar.

Ina zaton nan da ‘yan kwanaki kadan masu zuwa za mu kai ga yin hakan. Tuni na samu goyon bayan shugaba Xi Jinping, shi ma Firaminista Boris Johnson ya amince, kuma ina da tabbacin cewa shugaba Putin zai amince. Idan komai ya kammala za mu gudanar taro ta hoton bidiyo don tabbatar da hakan.

RFI :Ko ka yi magana da shugaba Putin a cikin ‘yan kwanakin nan?

Emmanuel Macron : Na yi magana da shi lokacin da aka bijiro da wannan batu. Amma daga lokacin da na samu kwarin guiwa daga sauran shugabanni, ban sake waiwayar sa ba, amma zan tuntube shi cikin sa’o’i masu zuwa.

RFI :Mai girma shugaban kasa muna godiya

Emmanuel Macron :Ni ma na gode sosai

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.