Saudiya-Coronavirus

Watakila a gudanar da aikin hajjin bana duk da coronavirus-NAHCON

Birnin Makkah na Saudiya
Birnin Makkah na Saudiya FETHI BELAID / AFP

Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON, ta ce, bayanan da ta samu daga Saudiya na nuna cewa, akwai yiwuwar gudanar da aikin hajjin bana, duk da cewa har yanzu duniya ba ta warke daga annobar coronavirus ba.

Talla

Shugaban Hukumar Alhazan Najeriya, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan ya sanar da haka a wata hira da ya yi da gidan rediyon tarayyar, wato FRCN.

Alhaji Hassan ya ce, bayanai daga Ma’aikatar Kiwon Lafiyar Saudiya ya yi hasashen cewa, watakila a  fara samun raguwar yaduwar coronavirus a Saudiya nan da ranar 21 ga watan Afrilu da muke ciki, kafin a yi nasarar kawar da cutar baki daya nan da watan Mayu a cewarsa.

Wannan ne ya bai wa Hukumar Alhazan Najeriya kwarin guiwar ci gaba da shirye-shiryenta na aikin hajjin bana kamar yadda ta sanar.

Gwamnatin Saudiya ta bukaci kasashen Musulmi na duniya da su jinkirta shirye-shiryen aikin hajjin bana har sai abin da hali ya yi saboda wannan annoba ta coronavirus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.