Amurka

Daruruwan Amurkawa sun bijire wa dokar zaman gida

Wani bangare na masu zanga-zangar adawa da zaman gida na dole a Texas na Amurka
Wani bangare na masu zanga-zangar adawa da zaman gida na dole a Texas na Amurka Reuters

Daruruwan mutane sun yi zanga-zanga a sassan biranen Amurka domin nuna adawa da dokar nan ta zaman gida na dole wadda aka kafa da zummar hana yaduwar cutar coronavirus.

Talla

Ana ganin masu zanga-zangar sun samu kwarin guiwa ne daga shugaban kasa Donald Trump da ke nuna adawarsa karara da ci gaba da tsawaita dokar zaman gidan.

Kimanin mutane 400 ne suka fito zanga-zangar duk da ruwan sama mai sanyi da ake tafkawa a New Hampshire, inda suka yi ta daga allunan dauke da sakwannin da ke cewa, "ba dole ba ne a killace jama’a a jihar da wannan annoba ba ta yi kamari ba."

Sauran wuraren da aka gudanar da zanga-zangar sun hada da Annapolis na Maryland, inda mutane 200 suka yi dandazo, yayin da fiye da 250 suka yi fitar-dango a birnin Austin na Texas.

Amurkawa kusan dubu 40 suka rasa rayukansu bayan fama da cutar coronavirus.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.