Canada

Dan bindiga ya harbe mutane 16 har lahira a Canada

Jami'an 'yan sandan Canada da suka yi nasarar kashe dan bindigar
Jami'an 'yan sandan Canada da suka yi nasarar kashe dan bindigar REUTERS/John Morris

Wani dan bindiga a cikin mota irin ta ‘yan sanda ya bude wuta tare da kashe mutane 16 a kasar Canada.

Talla

Maharin wanda aka bayyana sunansa a matsayin Gabriel Wortman mai shikaru 51 a duniya, ya share tsawon awanni 12 yana barin wuta a kan mutane kafin shi ma a bindige shi a lardin Nova Scotia.

Bayanai sun ce, tun ranar Asabar da ta gabata ne aka sanar da ‘yan sanda cewa, an fara jin karar harbi da Wortman ya yi a wani gari mai suna Portapique, kafin daga bisani a bindige shi a cikin daren da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI