Isra'ila-Falasdinawa

Falasdinu ta mayar da martani kan gwamnatin Isra'ila

Benny Gantz  da  Benyamin Netanyahu
Benny Gantz da Benyamin Netanyahu JACK GUEZ / AFP

Gwamnatin al’ummar Falasdinu ta yi kakkausar suka a game da abin da ta kira gwamnatin masu ra’ayin mamaya da ake shirin kafawa tsakanin Benyamin Netanyahu da Benny Gantz a Isra’ila.

Talla

Firaministan yankin Palasdinu Mohammed Shatayyeh ya bayyana gwamnatin da ake shirin kafawa a Isra’ila a matsayin wadda za ta kara tabbatar da kawo karshen duk wani fatan da ake da shi na samar kasashe biyu wato Isra’ila da Palasdinu da za su zauna kafada-da-kafada a tsakaninsu.

Wannan na zuwa ne bayan Netanyahu ya cimma wata yarjejeniya mai cike da tarihi da babban abokin hamayyarsa kuma kakakin Majalisar Dokokin Kasar,wato Beny Gantz domin gaggauta kafa gwamnatin hadaka, lamarin da zai kawo karshen rikicin siyasar kasar mafi muni da aka gani a baya-bayan nan.

Yarjejeniyar ta tsawon shekaru uku, za ta bai wa Netanyahu damar ci gaba da zama akan kujerar firaminista har tsawon watanni 18 nan gaba.

Sannan daga bisani shi ma Gantz zai dana kujerar ta  firaministan a tsawon watanni 18, inda daga nan kuma, za a gudanar da sabon zabe a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI