Coronavirus

COVID-19:Mata masu ciki da yara na cikin mummunan hatsari

Mata masu juna biyu da kananan yara na fuskantar hatsarin mutuwa sakamakon coronavirus
Mata masu juna biyu da kananan yara na fuskantar hatsarin mutuwa sakamakon coronavirus iStock / LSOphoto

Bankin Duniya ya yi gargadin cewa, annobar COVID-19 na iya haifar da karin mutuwar kananan yara da kuma mata masu ciki da kashi 45 a kasashe masu tasowa nan da karshen wannan shekara.

Talla

Binciken da wasu kungiyoyin kula da lafiya suka gudanar da aka wallafa a Mujallar Kula da Lafiya ta ‘The Lancet’ ya ce, muddin kasashe matalauta da ke nahiyar Afirka da Asiya da kuma kudancin Amurka suka gaza wajen samar da magunguna da iskar taimaka wa marasa lafiya numfashi da rigunan kare ma’aikatan lafiya da kuma tallafi, ana iya samun mutuwar a kalla yara miliyan guda da dubu 200 da kuma mata masu ciki 57,000 a cikin watanni 6 masu zuwa.

Daraktan Kula da Lafiya na Bankin, Dr Muhammaed Ali Pate ya ce annobar coronavirus na iya mayar da hannun agogo baya dangane da 'yan nasarorin da aka samu wajen harkar kula da lafiya.

Pate ya ce, muddin aka samu matsala wajen harkar kula da lafiya irin tashin hankalin da zai biyo mace-macen yara da mata zai tada hankalin duniya.

Ya zuwa yanzu nahiyar Turai da Amurka suka fi fuskantar illar cutar COVID-19 wajen samun mutane sama da miliyan 2 da suka kamu da cutar daga cikin miliyan 2 da dubu Dario 6 da ake da su a duniya.

A kasashe 45 na Afirka kuwa mutane 15,394 suka kamu da cutar, yayin da 716 suka mutu.

Stefan Peterson, jami’in UNICEF ya kara da cewar, ci gaba da yaduwar annobar COVID-19 babbar barazana ce ga rayuwar mata masu ciki da kananan yara saboda matsalar harkokin kula da lafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.