Ramadan

Azumi wata kafa ce ta magance coronavirus a duniya-Sheikh Uwais

Sheikh Abdullahi Uwais
Sheikh Abdullahi Uwais Facebook

Fitaccen malamin addinin Islama kuma mamba a Majalisar Bayar da Fatawa ta Najeriya, Sheikh Abdullahi Uwais ya bayyana cewa, azumin Ramadan wata kafa ce da Musulmi zai yi amfani da ita wajen kawar da annobar coronavirus wadda ta lakume rayukan mutane fiye da dubu 190 a sassan duniya.

Talla

A yayin zantawarsa da sashen Hausa na RFI, Sheikh Uwais ya ce, addu’a ce babbar gundunmawar da Msulumi zai bayar a irin wannan lokaci na coronavirus, musammam ma idan aka yi la’akari cewa, akwai addu’ar da duk mai azumi idan ya yi, Allah zai amsa a cewarsa.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakkiyar hirar Sheikh Uwais da RFI Hausa.

SHEIK ABDULLAHI UWAIS-RFI-HAUSA-2020-04-24

Azumin bana ya zo a cikin wani yanayi da kasashen duniya da dama suka hana taruwar jama’a a Masallatai don hana yaduwar coronavirus.

Wasu Musulmai na korafin cewa, hana su taruwa a Masallatai zai hana su gudanar da addu’o’in rokon Allah ya yaye annobar ta coronavirus.

Amma Sheikh Uwais ya bayyana cewa, wannan ba hujja ba ce, domin kuwa, Musulmai na iya gudanar da addu’o’insu a daidaikunsu ba tare da sun taru a wuri guda ba kuma Allah ya amsa.

Sheikh Uwais ya caccaki mutanen da ke karyata cutar coronavirus, yana mai cewa, ba su da wata hujja da suka dogara da ita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.