Coronavirus

Coronavirus ta lakume Amurkawa sama da dubu 3 a kwana daya

Wata katafariyar makabartar birnin New York na Amurka da ake binne mamatan da coronavirus ta kashe
Wata katafariyar makabartar birnin New York na Amurka da ake binne mamatan da coronavirus ta kashe Reuters

Annobar coronavirus ta yi sanadiyar mutuwar mutane dubu 186 da 462 a duniya tun farkon bullarta a watan Disamban bara a kasar China, inda a Amurka kadai, cutar ta kashe kusan mutane dubu 50, da suka hada da dubu 3 da 176 da ta kashe cikin sa'o'i 24 da suka gabata.

Talla

Sama da mutane miliyan 2 da  dubu 675 suka kamu da kwayar cutar a kasashen duniya 193, yayin da fiye da dubu 700 suka warke.

Baya ga kasar Amruka da ke sahun gaba wajen samun asarar rayuka, italiya ce ke  matsayi na biyu da asarar mutane  dubu 25 da 549 , sai kuma  dubu 23 da 157 da suka mutu a Spain, yayin da a Fransa, adadin mamatan ya kai dubu 21 da 856, sai kasar Birtaniya da ta yi asarar mutane dubu 18 da 738 a sanadiyar annobar ta coronavirus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.