Coronavirus ta halaka sama da mutane dubu 200

Wasu likitoci da suka dukufa wajen ceto rayuwar wadanda annobar coronavirus ta tagayyara.
Wasu likitoci da suka dukufa wajen ceto rayuwar wadanda annobar coronavirus ta tagayyara. Reuters

Alkalumman hukumomin lafiya sun ce jimillar adadin mutanen da annobar coronavirus ta halaka a sassan duniya a yanzu haka ya kai dubu 200 da 736.

Talla

Kididdigar hukumomin lafiyar ta kuma bayyana cewar cutar ta kama mutane miliyan 2 da dubu 864 da 70.

Daga cikin kusan mutane miliyan 3 da annobar ta harba, dubu 772 da 900 sun warke daga cutar.

Har yanzu Amurka ke matsayi na farko wajen fama da annobar, inda mutane dubu 53 da 70 suka mutu a kasar, sai Italiya mai mutane dubu 26 da 384 da suka mutu, sannan Spain mai mutane dubu 22 da 902.

A Faransa kuwa mutane dubu 22 da 614 annobar ta kashe, sai Birtaniya mai mutane dubu 20 da 319.

Daga cikin jimillar adadin mutanen dubu 200 da 736 da suka mutu a duniya, dubu 122 da 171, sun fito ne daga nahiyar Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.