WHO

Coronavirus na cigaba da halaka dubban mutane a sassan duniya

Wasu Musulmi yayin Sallah a wajen babban Masallacin Juma'a a Bangladesh na Baitul Mukkaram, dake babban birnin kasar Dhaka.
Wasu Musulmi yayin Sallah a wajen babban Masallacin Juma'a a Bangladesh na Baitul Mukkaram, dake babban birnin kasar Dhaka. AP Photo/Al-emrun Garjon

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, tace annobar coronavirus ta lakume rayukan mutane dubu 202 da 994 a fadin duniya, yayin da ta kama mutane kusan miliyan 3, wasu dubu 791 da 700 kuma sun warke.

Talla

Alkalumman da hukumar ta bayar a yau, sun ce har yanzu Amurka ke sahun gaba wajen yawan mutanen da annobar ta kashe da adadin dubu 53 da 934, sai Italiya da ta rasa mutane dubu 26 da 384, sannan Spain mai mutane dubu 23 da 190.

Faransa tayi asarar mutane dubu 22 da 614 sai kuma Birtaniya a matsayi na 5 bayan rasa mutane dubu 20 da 319.

Daga cikin mutane dubu 202 da 994 da suka mutu a duniya, dubu 122 da 846 sun fito ne daga nahiyar Turai, sai kuma dubu 56 da 450 daga Amurka da Canada, yayinda dubu 1 da 379 suka mutu a nahiyar Afirka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.