Gwamnatocin kasashe sun soma sassauta dokar hana zirga-zirga
Wallafawa ranar:
Gwamnatocin kasashen duniya sun fara daukar matakin janye dokar hana zirga-zirgar da suka kafa domin yaki da cutar coronavirus, inda a lahadin nan gwamnatin Spain ta baiwa yara kanana damar fita, karo na farko a cikin makwanni 6, inda aka ga yaran tare da iyayen su suna watayawa.
Su ma kasashen Faransa da Italiya da Amurka na shirin daukar matakai daban daban wajen cire dokar hana zirga-zirgar wadda ta shafi akalla rabin mutanen dake fadin duniya.
Saudiya ma ta bi sawun sauran kasashe kan dokar hana fitar, inda ta takaita dokar hana fita gida na sa’oi 24 da aka kafa domin yakar annobar coronavirus, sai dai umurnin bai shafi wasu garuruwa ba cikinsu harda birnin Makkah.
Gwamnatin Saudiyan tace daga yanzu dokar ta baiwa jama’a walwala tsakanin karfe 9 na safe zuwa karfe 5 na yamma, yayin da masu shaguna da ‘yan kasuwa zasu koma harkokin su daga ranar 13 ga watan gobe.
Sai dai birnin Makkah zai cigaba da zama cikin dokar hana fita na sa’oi 24.
Hukumar lafiya ta duniya tayi gargadi wajen ganin anyi taka tsan-tsan dangane da daukar matakin janye dokar da ta takaita zirga-zirgar, bayan karuwar adadin mutanen da cutar COVID-19 ta kama zuwa kusan miliyan 3 a fadin duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu