Sama da mutane dubu 797 sun warke daga cutar coronavirus - WHO

Wasu likitoci sanye da rigunan samun kariya daga cutar coronavirus a yankin Chennai dake kasar India.
Wasu likitoci sanye da rigunan samun kariya daga cutar coronavirus a yankin Chennai dake kasar India. REUTERS/P. Ravikumar/File Photo

Alkalumman hukumomin lafiya a yau litinin sun nuna cewa, yawan mutanen da annobar COVID-19 ta halaka a sassan duniya ya zarta dubu 206.

Talla

Hukumomin lafiyar na kasa da kasa sun ce a halin da ake ciki, annobar coronavirus ta halaka jimillar mutane dubu 206 da 567, tun bayan bullarta a China tare da yaduwa zuwa kasashe da manyan yankuna 193. Zalika yawan wadanda suka kamu da cutar ya zarta miliyan 2 da dubu 900.

Har yanzu Amurka ke kan gaba wajen fama da annobar ta coronavirus, bayan mutuwar mutane dubu 54 da 877 a kasar, sai Italiya da ta rasa mutane dubu 26 da 664, sannan Spain mai mutane dubu 23 da 521.

A Faransa annobar ta halaka mutane dubu 22 da 856 sai kuma Birtaniya a matsayi na 5 bayan rasa mutane dubu 20 da 732, sai dai ba a sanya mutanen da suka mutu a gidajen kulawa da tsofaffi ba cikin kidayar wadanda suka mutun a Birtaniyar.

Hukumar lafiya ta duniya WHO tace yawan wadanda suka warke daga cutar coronavirus a duniya ya karu zuwa sama da dubu 797.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.