Isa ga babban shafi
Amurka-WHO

Takaddama na barazanar sake kunno kai tsakanin Trump da Majalisa

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. REUTERS/Leah Millis
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman | Bashir Ibrahim Idris
1 min

Kwamitin majalisar wakilan Amurka dake kula da harkokin da suka shafi kasashen waje ya bukaci shugaba Donald Trump da ya gabatar musu da bayanai kan dalilin da ya sa ya katse tallafin kudaden da kasar ke baiwa Hukumar Lafiya Duniya WHO.

Talla

Kwamitin ya bukaci shugaban kasar ya gabatar da bayanan duk wasu tarurrukan da aka yi kafin daukar matakin daga watan Dosambar da ta gabata.

Kwamitin majalisar wakilan ta Amurka ya kuma soma nazari kan illa da matakin janye tallafin da Trump yayi zai yi kan yaki da annobar COVID-19.

Shugaban kwamitin Eliot Engel yace muddin fadar shugaban bata gabatar musu da takardun da suke bukata nan da ranar 4 ga watan mayu, zasu yi amfani da karfin da doka ta basu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.