Isa ga babban shafi
Duniya

WHO ta tuhumi gwamnatocin kasashe da yin sakaci kan coronavirus

Shugaban hukumar lafiya ta Duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus.
Shugaban hukumar lafiya ta Duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus. Fabrice COFFRINI / AFP

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta tuhumi kasashe da dama kan rashin daukar cutar coronavirus da muhimmanci, duk da tacewa hukumar ta yi kwakkwaran gargadi kan cutar da wuri.

Talla

Shugaban hukumar ta WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, yace tun a ranar 30 ga watan Janairun da ya gabata suka yi shelar bayyana cutar ta coronavirus a matsayin annoba kuma babbar barazana ga duniya, kuma a lokacin ba ta soma kisa a wajen kasar China ba, zalika mutane 82 kawai suka kamu da cutar a wajen kasar ta China, amma duk da haka wasu kasashe suka yi watsi da gargadin hukumar lafiyar.

Shugaban hukumar WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus

A farkon watan Afrilu nan shugaban Amurka Donald Trump ya caccaki hukumar ta WHO, bisa zarginta da gazawa wajen kare yaduwa annobar at COVID-19 zuwa sassan duniya, abinda ya sanya shugaban janye tallafin akalla dala miliyan 400 da yake baiwa hukumar lafiyar ta duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.