Duniya

Yawan wadanda suka kamu da cutar coronavirus ya zarta miliyan 3

Misalin fasalin taswirar duniya.
Misalin fasalin taswirar duniya. Reuters

Kididdigar hukumomin lafiya na kasa da kasa ta nuna cewar yawan mutanen da suka kamu da cutar coronavirus a fadin duniya ya zarta miliyan 3, kuma kusan kashi 80 na wadanda suka kamun na nahiyar Turai ne da Amurka. Yayinda annobar ta kashe sama da mutane dubu 209.

Talla

Alkalumman sun ce akalla mutane miliyan 3 da dubu 3 da 344 aka tabbatar cewa sun kamu da cutar ta coronavirus, yayinda kuma adadin wadanda annobar ta halaka a sassan duniyar ya kai dubu 209 da 388, mafi akasari a Turai, inda mutane miliyan 1 da dubu 393 da 779 suka kamu, dubu 126 da 233 kuma suka rasa rayukansu.

Har yanzu dai Amurka ke kan gaba wajen fuskantar kaifin annobar, bayan mutuwar mutane dubu 55 da 637 a kasar, daga cikin dubu 980 da 8 da suka kamu.

Italiya ke biye, wadda annobar ta halakawa mutane dubu 26 da 977 daga cikin dubu 199 da 414 da ta kama a kasar, sai Spain mai mutane dubu 23 da 521 da suka mutu, daga cikin dubu209 da 465 da suka kamu.

A Faransa annobar ta COVID-19 ta kashe mutane dubu 23 da 293, daga cikin dubu 165 da 842 da ta harba. Sai kuma Birtaniya da ta rasa mutane dubu 21 da 92, daga cikin dubu 157 da 149 da suka kamu da cutar.

A nahiyar Afrika anobar ta coronavirus ta halaka jimillar mutane dubu 1 da 458, daga cikin dubu 32 da 625 da suka kamu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.