Ba zamu zama sanadin barkewar yaki a Gabas ta Tsakiya ba - Iran
Wallafawa ranar:
Rundunar sojin Iran tace ba za ta zama sanadin barkewar yaki a yankin Gabas ta Tsakiya ba, duk da cewa a ‘yan watannin da suka gabata dangataka tayi tsami matuka tsakaninta da Amurka, musamman bayan kashe kwamandanta Qassem Soleimani da Amurkan tayi a Bagadaza, babban birnin kasar Iraqi.
Alwashin na Iran ya zo ne kwanaki kalilan bayan harba tauraron dan Adam na ayyukan soja da tayi zuwa sararin samaniya, da kuma barazanar mayar da kakkausan martani muddin sojin ruwan Amurka suka kaiwa jiragen ruwanta hari.
Wata sanarwa da sojin na Iran suka fitar, ta nuna cewar ba za su taba takalar fada ko kuma haddasa rikicin da zai shafi yankin Gabas ta Tsakiya ba, sai dai za su cigaba da kare kansu a duk lokacin da aka takale su.
Rundunar tace duk wata tsokana da barazana daga kowacce kasa, musamman Amurka zai gamu da martanin da ya dace.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu