Yawan rayukan da coronavirus ta lakume ya zarta dubu 217

Wasu jami'an lafiya a birnin New York dake Amurka. 24/4/2020.
Wasu jami'an lafiya a birnin New York dake Amurka. 24/4/2020. REUTERS/Lucas Jackson

Daga lokacin bullarta a karshen watan disambar da ya gabata a kasar China zuwa tsakiyar ranar yau laraba, annobar coronavirus ta kashe mutane dubu 217 da 439 a sassan duniya.

Talla

Sama da mutane milyan 3 da dubu dari daya da hudu ne cutar ta kama a kasashe 193, yayinda sama da dubu 859 suka warke daga cutar, kamar yadda alkalumman humomin lafiya na kasashe da kuma Hukumar Lafiya ta Duniya suka tabbatar.

A cikin sa'o'i 24 da suka gabata an samu karin mutane dubu 74 da 90 da suka harbu da wannan cuta, yayinda dubu 6 da 254 suka rasa rayukansu a sassan duniya.

Kasar Amurka ce dai inda annobar ta coronavirus tafi yin ta'adi, domin kuwa ta kashe mutane dubu 58 da 355 kafin tsakiyar ranar yau laraba, sai Italiya da cutar ta kashewa mutane dubu 27 da 359, yayinda Spain ta rasa mutane dubu 24 da 275.

Faransa ce kasa ta 4 a duniya ta annobar ta coronavirus tafi yiwa barna, inda ta yi awon gaba da rayukan mutane dubu 23 da 660, sai Birtaniya da ta rasa mutane dubu 21 da 678.

A Afrika, coronavirus ta kama mutane dubu 34 da 786, daga cikinsu kuma ta halaka dubu 1 da 526 a nahiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.