Coronavirus: Rayuka dubu 224 sun salwanta, dubu 889 kuma sun warke

Wasu jami'an lafiya a birnin Strasbourg na Faransa, yayin shirin tafiya da marsa lafiya 24. 3/4/2020.
Wasu jami'an lafiya a birnin Strasbourg na Faransa, yayin shirin tafiya da marsa lafiya 24. 3/4/2020. REUTERS

Sabbin alkalumman hukumomin lafiya sun ce cutar coronavirus, ta lakume sabbin rayuka dubu 6 da 337 cikin sa’o’i 24, abinda ya sanya a jimillar adadin mutanen da annobar ta halaka a fadin duniya kaiwa dubu 224 da 402.

Talla

Zuwa wayewar garin yau alhamis, sama da mutane miliyan 3 da dubu 141 da dubu 2 da 500 ne aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus, sai dai dubu 889 da 200 daga cikinsu sun warke.

Cikin sa’o’i 24 da suka gabata kuma annobar tafi yiwa Amurka barna inda ta halaka mata mutane dubu 1 da 913, sai Birtaniya da ta rasa mutane 795 da kuma Brazil mai mutane 474 a kwana 1.

Har yanzu dai wannan annoba tafi halaka rayuka a Amurka, inda a jimlace ta kashe mutane dubu 59 da 446, daga cikin mutane miliyan 1 da dubu 28 da 217 da suka kamu, akalla dubu 116 da 776 kuma suka warke.

A Italiya, mutane dubu 27 da 682 coronavirus ta halaka, sai kuma Birtaniya da yanzu ta koma kasa ta 3 a duniya da annobar tafi yiwa barna, bayan karuwar yawan mutanen da ta kashe mata daga dubu 21 zuwa dubu 26 da 97.

Spain ta rasa mutane dubu 24 da 275, sai Faransa mai mutane dubu 24 da 87, a Afrika kuma, coronavirus ta kashe mutane dubu 1 da 567.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.