WHO

Babu wata shaida dake nuna kirkirar coronavirus aka yi - WHO

Shugaban hukumar lafiya ta Duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus.
Shugaban hukumar lafiya ta Duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus. Christopher Black/WHO/Handout via REUTERS

Hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta sake cewar babu wata shaida dake nuna cewar an kirkiri cutar corona ce a dakin gwaje gwaje kamar yadda shugaban Amurka Donald Trump ke ta nanatawa.

Talla

Masana kimiya sun yanke hukuncin cewar cutar ta samo assali ne daga dabbobi a kasuwar sayar da namun daji dake Wuhan inda ta afka kan Bil Adama.

Michael Ryan, jami’in hukumar lafiya yace sun karbi sakamakon bincike daga masana da dama wadanda suka tababtar da cewar cutar ta Allah da Annabi ce, sabanin ikrarin shugaba Donald Trump.

Ryan yace abu mai muhimmanci shine gano assalin yadda cutar ta samu da kuma kokarin shawo kan ta wajen ganin an kaucewa samun haka nan gaba.

A nashi jawabi shugaban hukumar Tedros Adhanom Gebreyesus ya sake kare hukumar lafiyar daga zargin da ake mata cewar bata ankarar da duniya da wuri ba domin ganin an dauki matakin kariya.

Gebreyesus yace tun ranar 30 ga watan Janairu suka yi shelar dokar ta baci akan cutar, a dai dai lokacin da mutane 82 suka kamu da ita a wajen China ba tare da samun koda mutuum guda ya mutu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.