Amurka-China

Coronavirus ikon Allah ce ba tuggun dan Adam ba - Amurka

Wani inijiniya dauke da taswirar roba ta kyawar cutar coronavirus a birnin Beijing. 29/4/2020.
Wani inijiniya dauke da taswirar roba ta kyawar cutar coronavirus a birnin Beijing. 29/4/2020. AFP

Gamayyar daukacin hukumomin leken asiri ta Amurka, ta cimma matsayar cewa, annobar coronavirus da ta karade duniya, ta samo asali ne daga China, sai dai babu wani dan adam da ya kirkire cutar da gangan.

Talla

Gamayyar hukumomin leken asirin dai ta jima tana bada goyon baya ga mahukuntan kasar ta Amurka, da suka hada da wadanda ke yaki da annobar ta coronavirus ko COVID-19 wadda ta asamo asali daga China, kan zargin ko China na da hannu wajen sarrafa cutar.

Sanarwar da ofishin ya fitar, tace, wannan gamayya ta amince da ittifakin da masa kimiya suka yi na cewa, cutar ta COVID-19 ba wani dan adam ba ne ya kirkire ta ko kuma ya sauya mata halitta.

Wannan na zuwa ne bayan shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana kudirinsa na neman diyya daga kasar China, bisa zarginta da yin sakaci har annobar ta fantsama zuwa sassan duniya gami da tafka barnar halaka dubban rayuka, da karya tattalin arzikin kasashe.

Wasu a gefe guda dai na zargin cewar annobar da ta fara bulla daga kasuwar birnin Wuhan a China tana da alaka da jemage, yayinda wasu ke ganin, an sarrafa kwayar cutar ce daga dakin gwaje-gwajen kimiya da ke birnin.

Yanzu haka dai, wannan gamayya za ta ci gaba da sanya ido kan bayanan da ke fitowa, don gano ko cutar ta coronavirus ta fara yaduwa ne daga jikin dabba zuwa dan adam, ko kuma dai kukure aka samu a dakin gwaje-gwajen kimiya har cutar ta fantsama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.