Duniya

Coronavirus ta kashe rayuka sama da dubu 230 a kasashe 195

Tawagar likitoci yayin daukar wani da ya kamu da cutar coronavirus a tashar jiragen kasa ta Saint-Jean dake birnin Bordeaux a Faransa. 3/4/2020.
Tawagar likitoci yayin daukar wani da ya kamu da cutar coronavirus a tashar jiragen kasa ta Saint-Jean dake birnin Bordeaux a Faransa. 3/4/2020. AFP / Nicolas Tucat

Sama da mutane dubu 230 annobar coronavirus ta kashe a sassan duniya, daga farkon bullar wannan cutar zuwa tsakiyar daren ranar alhamis.

Talla

Alkalummab hukumomin lafiya na nuni da cewa, cutar wadda ta bulla cikin watan disambar bara a China, ta kama mutane milyan 3 da dubu 218 da 410 a kasashe 195.

Amurka ce inda annobar ta fi muni, bayan halaka mutane dubu 61 da 717, sai Italiya inda mutane dubu 27 da 967 suka mutu, yayinda a halin yanzu Birtaniya ke matsayin kasa ta uku da yawan mamata dubu 26 da 711.

A kasar Spain, coronavirus ta kashe mutane dubu 24 da 543, sai a makociyarta wato Faransa, inda cutar ta yi ajalin mutane dubu 24 da 376, yayinda wasu sama da dubu 1 suka mutu a Rasha.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kamfanonin samar da magunguna, da suka hada da Pfizer na Amurka, Biontech na Jamus da kuma AstraZeneca na Birtaniya ke cewa sun yi nisa wajen samar da allurar rigakafin wannan cuta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.