Amurka ta amince da Remdesivir a matsayin maganin coronavirus
Wallafawa ranar:
Shugaban Amurka Donald Trump yace hukumar kula da ingancin magunguna ta kasar, ta amince da a soma amfani da maganin Remdesivir kan cutar coronavirus.
Sanarwar da Trump yayi a wannan Juma’a, ta zo ne bayanda gwajin kwararru ya tabbatar da cewa maganin na Remdesivir zai iya magance cutar ta coronavirus, gami da rage tsawon lokacin da masu dauke da cutar ke dauka kafin murmurewa.
Kamfanin harhada magunguna na Gilead Sciences dake Amurka ne ya samar da maganin na Remdesivir, wanda a shekarun baya aka yi amfani da maganin wajen magance cutar Ebola, da wasu karin cututtukan masu kaifi.
Yayin sanar da nasarar gwajin maganin a ranar laraba 29 ga watan Afrilu, shugaban hukumar yaki da cututtuka ta Amurka Anthony Fauci, ce binciken da kwararru suka gudanar kan maganin na Remsesivir, ya nuna cewar, marasa lafiya ko masu dauke da cutar coronavirus da suka sha maganin, sun fi saurin samun waraka cikin sauki, sama da marasa lafiya da ba maganin suka sha ba.
Shugaban hukumar yaki da yaduwar cutukan ta Amurkan yace kimanin marasa lafiya dubu 1 da 90 ne suka bada damar yin gwajin sabon maganin akansu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu