Amurka

Trump yayi watsi da binciken masana kan asalin coronavirus

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. REUTERS/Leah Millis

Shugaban Amurka Donald Trump ya cigaba da jajircewa kan tuhumar China da kirkirar annobar coronavirus ko COVID-19 a dakin gwaje-gwajenta, wadda ta addabi duniya yanzu haka.

Talla

Yayin ganawa da menama labarai a farkon watan nan na Mayu, shugaban yace babu kuskure kan cewar da gangan China ta bar cutar ta yadu a duniya.

Shugaban Amurka Donald Trump kan zargin China da taka rawa wajen yaduwar annobar coronavirus

A baya bayan nan ne dai gamayyar daukacin hukumomin leken asiri ta Amurka, ta cimma matsayar cewa, annobar coronavirus da ta karade duniya, ta samo asali ne daga China, sai dai babu wani dan adam da ya kirkire cutar da gangan.

Wasu a gefe guda dai na zargin cewar annobar da ta fara bulla daga kasuwar birnin Wuhan a China tana da alaka da jemage, yayinda wasu ke ganin, an sarrafa kwayar cutar ce daga dakin gwaje-gwajen kimiya da ke birnin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI