Coronavirus

Coronavirus ta jefa Duniya cikin tsaka mai wuya - WHO

Daraktan sashin ayyukan agajin gaggawa na hukumar lafiya ta duniya WHO, Mike Ryan tare da shugaban hukumar ta WHO Tedros Adhanom Ghebereyesus a birnin Geneva na kasar Switzerland. 6/2/2020.
Daraktan sashin ayyukan agajin gaggawa na hukumar lafiya ta duniya WHO, Mike Ryan tare da shugaban hukumar ta WHO Tedros Adhanom Ghebereyesus a birnin Geneva na kasar Switzerland. 6/2/2020. REUTERS/Denis

Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya tace yayinda wasu kasashen duniya ke kokarin bude kofofinsu domin komawa harkokin yau da kullum da aka saba, cutar coronavirus za ta cigaba da zama barazana har sai an samu maganinta.

Talla

Babban jami’in hukumar Paul Ryan yace yayinda wasu kasashe yanzu haka ke fuskantar bala’in annobar, wasu sun yi nasarar shawo kan ta, abinda ke nuna fata mai kyau.

Ya zuwa yanzu dai mutane sama da miliyan guda sun warke daga cutar a fadin duniya daga cikin kusan miliyan 3 da rabi da suka kamu, sakamakon rawar da likitoci suka taka duk yake babu maganin cutar.

Ryan ya bayyana damuwa kan yadda cutar ke samun gurin zama a nahiyar Afirka da Amurka ta Kudu sakamakon karuwar mutanen dake kamuwa da ita.

Tun bayan barkewar cutar a China cikin watan Disambar bara, annobar ta fantsama zuwa kasashe da yankuna 210, yayinda kasashe irinsu China da Koriya ta Kudu da Singapore da New Zealand suka yi nasarar dakile ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.