Duniya

COVID-19 na gaf da lakume rayuka dubu 250 a duniya

Wasu jami'an lafiya dauke da mai fama da cutar coronavirus a birnin Minsk dake kasar Belarus.
Wasu jami'an lafiya dauke da mai fama da cutar coronavirus a birnin Minsk dake kasar Belarus. REUTERS/Vasily Fedosenko

Adadin mutanen da suka mutu sakamakon kamuwa da cutar COVID-19 a duniya ya kai dubu 245 da 576.

Talla

Sabbin alkalumman hukumomin lafiyar kasa da kasa sun nuna cewar, jumillar wadanda suka kamu da cutar ya kai miliyan 3 da dubu 479, sai dai daga cikinsu cikinsu kuma sama da miliyan guda da dubu 63 sun warke.

Annobar da ta bulla cikin watan disambar da ya gabata a kasar China, kawo yanzu ta bulla a kasashe da manyan yankuna 195 da ke sassan duniya.

Wani sabon batu da ya taso shi ne daidaiton jumillar alkalumman mutanen da annobar ta coronavirus ke halakawa, domin kuwa hukumar lafiya ta Duniya da sauran hukumomin lafiya na kasashe, na la'akari ne da mutanen da aka kwantar a asibiti sannan aka yi masu gwajin dake tabbatar da cewa sun harbu da kwayar cutar, yayinda a wasu kasashe rashin kayan aiki ke hana tantance jama’a.

A Amurka kawai, zuwa tsakiyar daren jiya lahadi coronavirus ta kashe mutane dubu 67 da 155, a Italiya mutane dubu 28 da 884 sai Birtaniya mai yawan mamata dubu 28 da 446.

Sauran kasashen da cutar ta fi yi wa ta'adi sun hada da Spain da ta rasa mutane dubu 24 da 264, sai Faransa mai mutane dubu 24 da 895 inda a Afrika COVID-19 ta kashe mutane dubu 1, da 701.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI