Muhalli

COVID-19 ta durkusar da kashi 80 na ayyukan hasashen aukuwar masifu a duniya

Wata mata tsaye a kusa da wata cibiyar hasashen Yanayi da Muhalli dake kan tsaunuka masu kankara na Helheim a kasar Greenland.
Wata mata tsaye a kusa da wata cibiyar hasashen Yanayi da Muhalli dake kan tsaunuka masu kankara na Helheim a kasar Greenland. AP

Majalisar Dinkin Duniya tayi gargadin cewa annobar coronavirus ko COVID-19, tayi tasiri matuka wajen durkusar da ayyukan sa ido kan muhalli, da sauyin yanayi, wadanda ake amfani da su wajen hasashen aukuwar masifu, ciki harda Ambaliyar ruwa da kuma, girgizar kasa.

Talla

A sabon rahoton da ta fitar, hukumar lura da hasashen yanayi ta majalisar dinkin duniya WMO, ta ce a halin da ake ciki, gwaje-gwajen yanayin da kwararru kan dauka ta hanyar amfani da jiragen sama ya ragu da akalla kashi 75 zuwa 80 cikin 100, sabanin yadda a kowace rana, kwararru kan yanayin da muhalli ke gudanar da gwaje-gwaje kan yanayin zafi ko sanyin iska, karfin gudunta da wasu fannonin sama da dubu 800 a fadin duniya.

Rahoton hukumar hasashen yanayin ta duniya, ya dora alhakin durkushewar ayyukan nata da na sauran kwararru dangane da Yanayin da Muhalli, kan yadda annobar COVID-19 ta tilasta dakatar da sufurin jiragen sama a fadin duniya da zummar dakile ta, abinda ya janyo durkushewar aikin daukar gwaje-gwaje da jiragen sama da kusan kashi 80.

Hukumar ta WMO, ta kuma yi gargadin cewa tasirin annobar ta COVID-19 bai bar hatta cibiyoyin hasashen yanayin dake aiki daga kasa ba, musamman a nahiyoyin Afrika, da Kudancin Amurka da Tsakiyarta, inda mafi akasarin cibiyoyin basu da karfin fasahar zamani.

A yanzu dai kwararru kan yanayin, da muhalli sun dogara ne kan taurarin da adam da ke kololuwar sararin samaniya da kuma na’urorin zamanin dake kasa masu sarrafa kansu, sai dai suma, majalisar dinkin duniya tace idan annobar coronavirus ta dauki lokaci tana ta’adi, rashin samun gyara, zai kassara su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI