Coronavirus

Dangote ya zuba naira biliyan 1.5 a asusun yaki da annobar corona - MDD

Hamshakin Attajirin Najeriya da nahiyar Afrika Alhaji Aliko Dangote a birnin Paris. 7/10/2016.
Hamshakin Attajirin Najeriya da nahiyar Afrika Alhaji Aliko Dangote a birnin Paris. 7/10/2016. AFP/Stéphane de Sakutin

Majalisar Dinkin Duniya tace Gidauniyar hamshakin attajirin Najeriya Aliko Dangote ta zuba kudin da ya kai naira biliyan guda da rabi cikin asusun yaki da annobar coronavirus wadda ke cigaba da lakume rayukan jama’a a fadin duniya.

Talla

Majalisar tace wannan hadin kai tsakanin Gidauniyar Dangote da Majalisar zai taimakawa gwamnatin Najeriya sosai wajen karfafa bangaren kula da lafiya da kuma taimakawa wadanda suka kamu da cutar wajen samun kular da ta dace.

Majalisar tace za’ayi amfani da wadannan kudade wajen sayan kayayyakin kula da lafiya da aka fi bukata da suka shafi kayan gwaji da na’urorin aiki domin yaki da cutar COVID-19.

Shugaban Gidauniyar Aliko Dangote yace illar da cutar COVID-19 ta shafi kowa kuma babu wani bangare da zai shawo kan ta shi kadai, abinda ya sa ya zama wajibi ga kungiyoyi masu zaman kan su su bada gudumawa domin yaki da wannan abokiyar gaba.

Dangote yace bukatar su itace marawa gwamnati baya yaki da cutar da kuma tabbatar da ganin an dakile ta.

Yayin da yake karbar gudumawar Babban jami’in Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya Edward Kallon yace Najeriya zata samu nasarar yaki da annobar COVID-19 ne kawai idan kowa ya bada gudumawa wajen taimakawa kokarin da gwamnati keyi.

Bayan sanya hannu wajen hadin kai da Majalisar Dinkin Duniya Gidauniyar Dangote ta bada gudumawa sosai ga Jihohin Lagos da Kano wajen shawo kan wannan annoba wadda ta kashe mutane 103 a Najeriya bayan ta kama mutane sama da 3,000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.