Coronavirus

MDD ta yi shelar neman karin dala biliyan 4.7 don yakar corona

Zauren Majalisar Dinkin Duniya dake birnin New York.
Zauren Majalisar Dinkin Duniya dake birnin New York. REUTERS/Shannon Stapleton

Majalisar Dinkin Duniya ta sake kaddamar da wata sabuwar gidauniya ta kusan dala biliyan 5 domin ceto miliyoyin rayukan jama’a sakamakon annobar COVID-19 ko coronavirus dake cigaba da lakume rayuka a kasashe matalauta.

Talla

Sabuwar gidauniyar ta saba da ta dala biliyan 2 da Majalisar ta fara kaddamarwa domin aikin jinkai a ranar 25 ga watan Maris, wadda ta samu kusan rabin kudin.

Shugaban hukumar jinkai na Majalisar Mark Lowcock, yace muddin aka gaza wajen daukar matakan gaggawa don taimakawa, kasashe matalauta za su fuskanci matukar illa dangane da wannan annoba wadda babu ruwanta da yunwa ko talauci.

Daga cikin kasashen da ake sa ran za su amfana da tallafin akwai Jamhuriyar Benin da Djibouti da Liberia da Mozambique da Pakistan da Philippines da Saliyo da Togo sai kuma Zimbabwe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.