Coronavirus na cigaba da halaka dubban rayuka a duniya

Wata tashar jiragen kasa ta karkashin kasa a Shanghai dake China. 2/3/2020.
Wata tashar jiragen kasa ta karkashin kasa a Shanghai dake China. 2/3/2020. REUTERS/Aly Song

Alkalumma na baya-bayan nan da hukumomin lafata na kasashe suka fitar, sun nuna cewa annobar COVID-19 ta kashe mutane kusan dubu 267 daga watan disamba zuwa daren ranar Alhamis a sassan duniya.

Talla

Akalla mutane miliyan 3 da dubu 806 da wasu mutanen 440 ne suka harbu da kwayar cutar a kasashen duniya 195, yayinda miliyan 1 da dubu 170 da kusan mutane 100 suka warke daga cutar, kamar dai yadda sahihan alkaluma na wadanda aka yi wa wani suka tabbatar.

A cikin sa'o'i 24 da suka gabata COVID-19 ta kashe mutane da dama, domin a Amurka kawai an samu mamata dubu 2 da 862, sai Brazil mai mutane 615, sannan Birtaniya inda mutane 539 suka rasu cikin kwana guda.

A game da irin ta'adin da ta yi daga farkon bullarta a watan disamba zuwa tsakiyar daren jiya Alhamis, Covid-19 ta kashe mutane dubu 74 da 844 a Amurka, dubu 30 da 615 a Birtaniya, sai kuma Italiya inda wasu dubu 29 da 958 suka rigamu gidan gaskiya.

A Spain yawan mamatan ya tashi zuwa dubu 26 da 70, a Faransa mutane dubu 25 da 987 ne aka tabbatar da cewa sun mutu kafin tsakiyar daren na jiya, yayin da a Afrika coronavirus ta kasance ajalin mutane dubu 2 da 65 kawo yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.