Majalisar Dinkin Duniya

Guterres ya bukaci shugabannin addinai su yaki labaran karya

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres. REUTERS/Tiksa Negeri

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci shugabannnin addinai da su kalubalanci labaran karya da sakonnin batanci dake haifar da rikice-rikicen addini, da bata suna da kalamun nuna kyama, a daidai lokacin da annobar coronavirus ta yi wa duniya kawanya.

Talla

A sakon gargadi da ya aikewa shugabannin addinan ta bidiyo Guterres ya janyo hankalin su kan shawo kan kalubalen COVID-19 da masu tsatsauran ra’ayi da kungiyoyi ke kokarin amfani da shi domin bijirewa shugabanni da kuma kawar da hankalin jama’a wajen biyan bukatun kan su.

Sakataren ya bukaci shugabannin da su fifita kira domin hadin kan jama’a wajen kare hakkin Bil Adama da mutuncin sa da kuma hadin kai da fahimta da kuma mutunta jina.

Guterres yace shugabannin addinai na iya taka rawa wajen shugabanci na gari a cikin al’ummar su da wajen ta hanyar shawo kan annobar da ake fuskanta da kuma warkewa, yayin da suke fahimtar da mutane bukatar kaucewa tashin hankali da nuna kyama da wariyar jinsi da duk wata hanyar tada hankali.

Sakataren ya kuma bukaci kawo karshen cin zarafin mata da ‘yam mata a daidai lokacin da ake fuskantar illar annobar COVID-19, inda ya bukaci shugabannin addinan dasu daga muryar su wajen Allah wadai da irin wannan hali da kuma yada bukatar hadin kai, nuna kauna da mutunta juna.

Taron wanda Jakadan Morocco dake Majalisar Dinkin Duniya Omar Hilale ya shirya, ya samu halartar shugabannin mabiya darikar Katolika da Yahudawa da kuma Musulmai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.