Coronavirus

Rayukan mutane sama da dubu 290 sun salwanta saboda COVID-19

Wasu jami'an lafiyar kasar Korea ta Kudu tare da mai dauke da cutar coronavirus.
Wasu jami'an lafiyar kasar Korea ta Kudu tare da mai dauke da cutar coronavirus. AFP

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon annobar COVID-19 a duniya ya zarce 290,000, yayinda wadanda suka kamu da cutar suka zarce miliyan 4 da dubu 200, kuma miliyan guda da dubu 444,700 sun warke.

Talla

Alkaluman da hukumar lafiya ta gabatar daren jiya sun ce mutane 290,477 suka harbu da cutar a fadin duniya, kuma 159,205 sun fito ne daga nahiyar Turai, yayin da Amurka ke da mutane 82,105.

Daga cikin wannan adadi na duniya, Birtaniya na da yawan mutane 32,692 da suka mutu, Italia na da 30,911, Faransa na da 26,991 sai kuma Spain mai mutane 26,920.

A cikin sa’oi 24 da suka gabata, mutane 5,184 suka mutu a duniya, yayin da aka samu sabbin mutane 77,733 da suka kamu da cutar.

Kasar Rasha yanzu ita ce kasa ta biyu da ta fi yawan mutanen da suka kamu da cutar, inda yawan su yak ai 232,000, bayan Amurka mai mai yawan mutane miliyan guda da 358,000.

Ya zuwa wannan lokaci an tabbatar da mutane 68,364 sun kamu da cutar a Afirka, kuma 2,376 sun mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI