Lafiya

Annobar COVID-19 ka iya haddasawa dubban mutane tabin hankali - Guterres

Antonio Guterres, Sakataren Majalisar Dinkin Duniya.
Antonio Guterres, Sakataren Majalisar Dinkin Duniya. TONY KARUMBA / AFP

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, yayi gargadin cewar annobar coronavirus na iya haifar da gagarumar matsalar rashin lafiyar da ta shafi tabin hankali, inda ya bukaci daukar mataki domin kawo karshen irin illar da cutar ta haifarwa jama’a.

Talla

Guterres yace yayinda kare lafiyar jama’a ya zama abin mayar da hankali a watannin farko na samun wannan annoba, cutar ta kuma jefa dimbin jama’ar duniya cikin wani yanayi na matsalar tabin hankali.

Sakataren yace bayan kwashe shekaru masu yawa ana kauda kai wajen zuba jari a harkar kula da lafiya da kula da masu fama da rashin lafiyar da ta shafi tabin hankali, yanzu haka cutar COVID-19 na illa ga iyalai da al’ummomi da kuma sanya musu matsalar kwakwalwa.

Guterres yace koda an shawo kan annobar coronavirus, bakin ciki da damuwa da kuma fuskantar koma bayan da ta shafi harkar lafiya za su cigaba da shafar jama’a da al’ummomi.

Wannan matsayi na Majalisar Dinkin Duniya ya dada fito da fargabar da mutane ke da ita na kamuwa da cutar ko kuma wani da suke kauna ya kamu da ita, ko kuma su mutu daga coronavirus wadda ta kashe mutane kusan 300,000 a fadin duniya tun bayan bullarta daga kasar China a karshen shekarar 2019.

Matsayin Majalisar ya kuma dada fito da illa da fargabar da miliyoyin mutane ke da ita na rasa ‘yan uwansu sakamakon annobar COVID-19 ko fargabar rasa hanyar cin abincinsu, da kuma irin halin da suka shiga lokacin da aka tilasta musu zaman gida.

Devora Kestel, shugabar sashin dake kula da masu fama da tabin hankali a Hukumar Lafiya ta Duniya, tace suna da masaniyar cewar fargaba da rashin tabbas da matsalar tattalin arziki sun haifar da damuwar da kan haifar da matsalar da sukan shafi kwakwalwa.

Kestel tace su kansu ma’aikatan kula da lafiya da masu taimaka musu na fuskantar irin wannan yanayi, saboda irin halin da suka shiga wajen kula da tarin mutanen da suka kamu da wannan annoba, wadda ya haifar da kisan kai tsakanin wasu ma’aikatan, yayinda sauran jama’a suma suke fuskantar irin wannan yanayi saboda halin firgicin da suka shiga.

Jami’ar tace su kansu yaran da aka hana zuwa makaranta na fuskantar irin wannan damuwa da ta shafi tababa da rashin tabbas, yayinda mata ke fuskantar matsalar cin zarafi a cikin gidajensu sakamakon yadda gidajen suka cika da jama’a saboda dokar hana fita gida.

Kestel tace mutane masu yawan shekaru ko kuma dattijai tare da masu fama da wata matsalar da ta shafi rashin lafiya na sahun gaba, wajen ganin irin matsalolin da aka zayyano yayinda suke fuskantar barazanar kamuwa da cutar coronavirus.

A karshe Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci kasashen duniya da su sanya hanya mai sauki wajen samun taimako ga masu fama da irin wadannan matsaloli, da kuma matakan gaggawa ga masu fama da matsalar da ta shafi kwakwalwa a cikin shirinsu na tinkarar wannan annoba tacoronavirus da ta addabi duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.