Duniya

Shugabannin duniya sun bukaci samar da rigakafin corona kyauta

Daya daga cikin kwararru cibiyar binciken kimiyya ta Cobra Biologics dake Birtaniya. 30/4/2020.
Daya daga cikin kwararru cibiyar binciken kimiyya ta Cobra Biologics dake Birtaniya. 30/4/2020. Reuters

Shugabannin kasashen duniya na da, da na yanzu, sun bukaci samar da riga-kafin cutar coronavirus kyauta ga kowa.

Talla

Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa da Fira Ministan Pakistan Imran Khan, na cikin sama da mutane 140 da suka sanya hannu a cikin wata wasika da ke cewa, ya kamata a bayyana riga-kafin coronavirus a fili, sannan kuma a samu musayar bayanai tsakanin masana kimiya na kasa da kasa.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ke shirin gudanar da babban taronta na shekara-shekara nan da mako mai zuwa, yayinda mutanen da suka rattaba hannu kan wasikar, suka bukaci Hukumar Lafiyar da ta mayar da hankali kan batun samar da riga-kafin kyauta ga kowa.

Zalika shugaban kasar Senagal, Makky Sall da takwaransa na Ghana Nana Akufo Addo, da tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, na cikin fitattun mutanen da suka sanya hannu kan wannan wasika.

Wasikar dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake tayar da jijiyoyin wuya a Faransa, bayanda babban kamfanin sarrafa magunguna na kasar da ake kira Sanofi, yace zai yi tanadin jigilar farko ta riga-kafin cutar coronavirus ga Amurka saboda yadda gwamnatin Amurkar ke tallafawa aikin gudanar da bincike kan riga-kafin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.