Amurka-Coronavirus-China

Ba na fatan sake yiwa shugaban China magana - Trump

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. MANDEL NGAN / AFP

Shugaban Amurka Donald Trump, yace ba ya fatan sake yin magana da takwaransa na China Xi Jinping inda a fakaice ma yake cewa abu ne mai yiwuwa ya yanke duk wata alaka da kasar ta China, saboda takun sakar da kasashen ke yi da juna dangane da batun Coronavirus.

Talla

Trump ya bayyana haka ne, yayin zantawa da tashar talabijin ta ‘Fox Business’ inda yace a halin yanzu yana cikin fushi a game da halayen mahukuntan kasar ta China, kuma akwai hanyoyi da dama da zai iya daukar fansa akansu, ciki harda katse kowace irin hulda da kasar.

Yanzu haka dai Trump ya share makwanni yana tuhumar China da kirkirar cutar coronavirus daga dakin gwaje-gwajenta a birnin Wuhan, duk da cewa kasar ta China na cigaba da musanta zargin, zalika bincikin tawagar kwararrun hukumomin liken asirin Amurka ya nuna cewa, babu hannun dan adam wajen kirkirar cutar ko kuma sauya mata halitta.

Trump ya share makwanni yana tuhumar China da kirkirar cutar coronavirus daga dakin gwaje-gwajenta a birnin Wuhan, duk da cewa kasar ta China na cigaba da musanta zargin, zalika binciken tawagar kwararrun hukumomin leken asirin Amurka ya nuna cewa, babu hannun dan adam wajen kirkirar cutar ko kuma sauya mata halitta.

Bayaga halaka dubban rayukan da take yi, annobar ta coronavirus ko COVID-19 na cigaba da kassara tattalin arzikin kasashen duniya, abinda ya janyo durkushewar fannonin sufuri, kasuwanci, zuba hannayen jari, wasanni har ma da ayyukan hasashen kimiyya don gano yiwuwar aukuwar masifu a duniya da suka hada da girgizar kasa, da ambaliyar ruwa.

Bangaren kwadago ma dai bai tsira ba, domin tuni miliyoyin mutane suka rasa guraben ayyukan yi, yayinda sana’o’in wasu miliyoyin a kasashe masu tasowa, talauci da ma wadanda suka cigaba suka durkushe.

Babban misali shi ne, sabon rahoton da ma’aikatar kwadagon Amurka ta fitar a ranar Alhamis 14 ga watan Mayu, wanda ya nuna cewar a karshen makon da ya kare, an samu karin Amurkawa miliyan 2 da dubu 980 ne suka rasa guraben ayyukansu, sakamakon annobar coronavirus dake cigaba da tagayyara tattalin arzikin kasar.

Karin mutanen ya sanya jumillar adadin Amurkawan da suka rasa ayyukansu dalilin tasirin annobar ta COVID-19 kaiwa miliyan 36 da dubu 500.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.