Mu Zagaya Duniya

Bitar muhimman abubuwan da suka faru a makon jiya

Sauti 19:51
Hoton taswirar duniya dake nuna sassan da annobar coronavirus ta mamaye.
Hoton taswirar duniya dake nuna sassan da annobar coronavirus ta mamaye. European pharmaceutical review

Kamar yadda aka saba a kowane mako, sashin Hausa na RFI kan waiwaye kan wasu daga cikin muhimman labaran da suka fi daukar hankulan duniya a cikin makon da ya kawo karshe. A wannan karon, Garba Aliyu Zaria ya soma bitar muhimman labarun ne daga birnin Kabul na Afghanistan, inda 'yan ta'adda suka kai mummunan hari kan wani asibitin kungiyar likitoci ta kasa da kasa MSF.