Amurka-WHO

Mai yiwuwa Trump ya janye matakin daina tallafawa hukumar WHO

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. Brendan Smialowski / AFP

Shugaban Amurka Donald Trump yace yana nazarin matakin da ya dauka na daina baiwa Hukumar Lafiya ta Duniya kudade, amma zuwa yanzu bai yanke hukunci kan matakin da zai dauka ba.

Talla

A sakon da ya aike ta kafar twitter, Trump yace cikin matakan da yake nazari akai harda baiwa hukumar akalla kasha 10 na kudin da Amurka ta saba baiwa Hukumar a matsayin gudumawa.

Shugaban da ya zargi hukumar da rufa rufa dangane da bayanan da suka shafi barkewar annobar COVID-19, ya sanar da dakatar da kudaden da Amurka ke bata a matsayin tallafin gudanar da ayyukanta, inda ya bukaci sake nazari kan sha’anin gudanarwar hukumar.

Kafar yada labaran Fox dake Amurka ta ruwaito cewar ta ga wasikar gwamnatin Amurka dake bayyana shirin shugaba Trump na cigaba da baiwa hukumar lafiyar ta WHO kudade.

Amurka ce kasar da tafi baiwa Hukumar kudade, inda a kowacce shekara take bada kusan dala miliyan 400.

A wannan mako mai kamawa ake sa ran Hukumar Lafiyar ta gudanar da taronta na shekara-shekara wanda zai janyo kwararu daga sassan duniya da kuma ministocin lafiya daga kasashe kusan 200.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.