Duniya-WHO

Coronavirus: Hukumar lafiya ta Duniya na taron kwararru na kasa da kasa

Shugaban hukumar lafiya ta Duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus.
Shugaban hukumar lafiya ta Duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus. UN Photo/Eskinder Debebe

Yau Hukumar Lafiya ta Duniya take fara gudanar da taron ta na shekara shekara wanda ke baiwa masana harkar kula da lafiya da shugabannin hukumar da shugabannin kasashe, da kuma ministocin lafiyarsu damar tattauna batutuwan da suka shafi kiwon lafiya da kuma annobar da ake samu.

Talla

Taron na bana na zuwa ne a daidai lokacin da duniya ke fama da annobar COVID-19, yayin da Amurka da China ke takun saka kan bote bayanan cutar, matsalar da ta shafi Hukumar ta duniya.

Shidai wannan taro na Hukumar Lafiya da aka saba kwashe makwanni 3 ana gudanar da shi, a wannan karon za a dauki kwana biyu ne kacal, saboda annobar COVID-19 wadda ta kashe mutane sama da 310,000, ta kuma hana zirga-zirga.

Barkewar cutar COVID-19 da kuma yadda kasashen duniya suka tinkari matsalar da batun samun maganin rigakafi da kuma rarraba shi ake saran zai mamaye taron, yayin da masana kimiya ke ta raba dare wajen ganin sun samu nasara.

Zargin da Amurka ke yiwa China na boye bayanan annobar COVID-19 da kuma yadda take samun goyan bayan Hukumar Lafiya na iya haifar da tarnaki wajen daukar duk wani matakin bai daya, ganin yadda kasashen ke cacar baki a tsakanin su.

Sai dai kafin fara taron, shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewar yana nazarin baiwa Hukumar lafiya kudaden da kasar ta saba bata, wanda ya katse a watan jiya, saboda zargin hukumar cewar tana marawa China baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.