Isra'ila

Sabuwar gwamnatin Isra'ila za ta cigaba da mamaye yankin Falasdinawa - Netanyahu

Fira Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu tare da tsohon abokin hamayyarsa Benny Gantz, bayan kafa sabuwar gwamnatin hadin giwa. 17/5/2020.
Fira Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu tare da tsohon abokin hamayyarsa Benny Gantz, bayan kafa sabuwar gwamnatin hadin giwa. 17/5/2020. ADINA VALMAN / KNESSET SPOKESPERSON OFFICE / AFP

Majalisar Dokokin Isra’ila ta rantsar da sabuwar gwamnatin-hadaka karkashin jagorancin Fira Ministan kasar, Benjamin Natanyahu da tsohon abokin hamayyarsa Benny Gantz, lamarin da ya kawo karshen rikicin siyasa mafi tsawo a kasar.

Talla

Bayan sama da kwanaki 500 ba tare da tsayayyar gwamnati ba, majalisar dokokin Isra’ila mai kujeru 120, ta amince da kafa gwamnatin hadakar kasar da za ta shafe tsawon shekara uku ta jagoranci.

Mambobin Majalisar 73 ne suka kada kuri’ar amincewa da gwamnatin hadakar, yayinda 49 suka nuna adawa, inda kuma mutum guda ya kauracewa zaman kada kuri’ar.

Sabuwar gwamnatin dai za ta fuskanci matsaloli a makwanninta na farko, da suka hada da koma-bayan tattalin arziki sakamakon cutar coronavirus, da kuma wani gagarumin rikici da ke tafe dangane da mamaye wani bangare mai yawa na yankin Falasdinawa dake Yamma da Kogin Jordan.

A yayin gabatar da jawabi a zauren majalisar dokokin, Fira Ministan Netanyahu yace, sabuwar gwamnatin hadakar za ta fadada ikonta da mulkinta kan Yahudawa ‘yan share wuri zauna a yankin Yamma ga Kogin Jordan.

Sai dai ana ganin wannan matakin zai haddasa kumfar-baki tsakanin kasashen duniya tare da rura wutar rikici a yankin na Yamma da Kogin Jordan, inda ya kasance matsuguni ga Falasdinawa akalla miliyan uku, da kuma wasu Isra’ilawa dubu 400 da suka yi kane-kane a wuraren, abinda ya sabawa dokokin kasa da kasa.

Sai dai Netanyahu yace matakin nasa ba zai hana zaman lafiya ba ko kadan, hasali ma zai kara hada kawunansu da Falasdinawa ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.