China-Coronavirus

Gwajin maganin coronavirus kan dabba yayi nasara a matakin farko - China

Wasu kwararrun masu binciken kimiyya a dakin gwaje-gwaje na Jami'ar Peking dake Beijing, babban birnin kasar China. 14/5/2020
Wasu kwararrun masu binciken kimiyya a dakin gwaje-gwaje na Jami'ar Peking dake Beijing, babban birnin kasar China. 14/5/2020 Wang Zhao / AFP

Masana kimiya a China sun ce yanzu haka sun dukufa kan aikin samar da maganin da ke da karfin kawo karshen annobar coronavirus.

Talla

Kwararrun dai sun yi amanna cewar, sabon maganin da suka kokarin samarwa, zai kashe kwayar cutar ba tare amfani da wani riga-kafi ba.

Maganin da ake gwajinsa a Jami’ar Peking ta China na da karfin gaggauta warkar da mutanen da suka harbu da cutar coronavirus, sannan kuma ya baiwa garkuwar jikinsu kariyar wucen-gadi daga kwayar cutar, kamar yadda masana kimiyar da ke bincike suka bayyana.

Sunney Xie, darakta a cibiyar binciken kwayoyin halittu a Jami’ar ta birnin Beijing, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, tuni wannan maganin ya samu nasara a matakin gwaji kan dabbobi.

Xie ya ce, sun yiwa wasu beraye allurar kashe kwayoyin cuta, inda bayan kwanaki biyar, tarin kwayoyin cutar da ke jikin berayen ya ragu matuka, abin da ke nuna cewa, wanann maganin na da tasirin warkar da mara lafiya.

Daraktan ya ce, tawagarsa na aiki dare da rana wajen bincike kan maganin kashe kwayoyuin cutar, kuma nan da wani lokaci a cikin wannan shekara, za a kammala harhada maganin domin fara amfani da shi a cewarsa.

Ana sa ran fara gwajin maganin a Australia da wasu kasashen duniya, lura da cewa, tuni masu dauke da coronavirus suka ragu a China.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.