Duniya-Coronavirus

WHO ta amince da kudurori 5 na magance matsalar kiwon lafiya a duniya

Shugaban hukumar lafiya ta Duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus.
Shugaban hukumar lafiya ta Duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus. AFP

Taron hukumar Lafiya ta Duniya da aka kammala a jiya Talata, ya amince da wasu kudurori guda biyar, wadanda ake sa ran za su a kawo karshen kalubalen da sha’anin lafiya ke fuskanta a fadin duniya.

Talla

Taron da ya shafe kwanaki 2 yana gudana a karkashin jagorancin hukumar WHO da kasashe manbobinta, ya maida hankali ne kan annobar coronavirus da ta addabi duniya a yanzu haka.

A karshen taron gwamnatocin kasashe da hukumar lafiyar sun cimma matsayar aiwatar da sauye-sauye kan fannonin sha’anin lafiya, da suka hada da yiwa tsarin daukar matakan dakile yaduwar cutuka garambawul, sauya fasalin tsarin ayyukan hukumar lafiyar ta duniya, da kuma gudanar da sabon bincike mai zaman kansa kan asalin kwayar cutar coronavirus, kokarin gano ko an taimaka wajen yaduwarta da gangan, ko kuma sakaci aka yi wajen daukar matakan dakile ta tun a matakin farko.

Sauran kudurorin sun hada da gaggauta samar da magani da rigakafin cutar ta coronavirus, sai kuma bukatar daga darajar Taiwan zuwa jerin kasashen dake sa ido kan ayyukan hukumar lafiya ta duniya WHO, batun da taron ya jinkirta yanke shawara akai har zuwa karshen shekarar 2020 da muke ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.