Saudiya-Daular Larabawa

Saudiya da Hadaddiyar Daular Larabawa sun bada umarnin yin Sallar Idi a gida

Masallacin Harami dake birnin Makkah.
Masallacin Harami dake birnin Makkah. AFP / Getty Images

Hukumomin Saudiya da na Hadaddiyar Daular Larabawa sun ce Masallatai a kasashen za su cigaba da kasancewa a rufe, abinda ke nufin al’ummar Musulmi a kasashen za su gudanar da Sallar Idi karama ta bana a gida tare da iyalansu.

Talla

Gwamnatocin kasashen sun bayyana daukar matakin a matsayin hanyar dakile yaduwar annobar coronavirus, bisa shawarwarin kwararru a fannin lafiya.

Annobar coronavirus da a yanzu haka ke addabar duniya bayan halaka sama da mutane dubu 332 daga cikin sama da miliyan 5 da ta kama, ta tilastawa hukumomin Saudiya soke gudanar da Sallar Tarawih a Masallatan Haramin Makkah da Madina, don kaucewa bazuwar cutar.

A bangarenta, bayaga soke Sallar Idi a Masallatai, Hadaddiyar Daular Larabawa ta sanar soke dukkanin hada-hadar murnar Sallar ta bana dake hada cinkoso, ciki harda ziyara tsakanin ‘yan uwa da abokan arziki, duk dai don dakile yaduwar annobar coronavirus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.