Amurka

Trump na neman hargitsawa kasashen Turai lissafi kan tsaro

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. REUTERS/Leah Millis

Kasashen dake cikin kungiyar tsaro ta NATO sun kira taron gaggawa, bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da janyewar kasar daga yarjejeniyar tsaron da ake kira da suna ‘Open Skies’, yayinda Rasha ta ce matakin zai jefa sha’anin tsaron yankin turai a cikin hadari.

Talla

Tuni dai ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas ya bukaci Amurka da ta sake tunani kafin daukar matakin, sai dai Amurka ta ce za ta janye ne saboda ta gano cewa tun da jimawa Rasha ta daina mutunta yarjejeniyar da aka kulla kimanin shekaru 18 da suka gabata.

Yarjejeniyar ta ‘Open Skies’ dai ta bada damar tattara bayanan tsaro da sinitiri a sararin samaniyar kasashen da suka rattaba hannu akanta.

Zalika karkashin wannan yarjejeniya, ya zama wajibi kasashen da suka rattaba ma ta hannu su rika bayar da haske a game da kai da kawon da sojojinsu ke yi, tare da takaita gasar kera makamai a tsakaninsu.

Amurka ta ce a shirya take ta shiga tattaunwa da sauran kasashe domin yi wa yarjejeniyar gyara, lura da cewa wani bangarenta ya nuna cewa za a iya janyewa daga cikinta ne bayan watanni 6.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.