Amurka

Trump ya baiwa gwamnonin Amurka umarnin bude wuraren ibada nan take

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. REUTERS/Leah Millis

Shugaban Amurka Donald Trump ya baiwa gwamnonin jihohin kasar umarnin bude dukkanin wuraren Ibada na Masallatai da Mujami’un, wadanda a baya aka rufe saboda annobar coronavirus.

Talla

Trump ya bada umarnin ne a yau Juma’a, yayin taron manema labarai a fadar gwamnatinsa ta White House dake birnin Washington.

A cewar shugaban na Amurka ya zama dole gwamnonin kasar su yi abinda ya dace wajen bude muhimman wuraren Ibadar nan take a karshen makon nan.

Trump yayi gargadin cewar, idan har gwamnonin suka saba umarninsa, to zai yi amfani da karfin ikon da tsarin mulki ya bashi, wajen tilasta bude Mujami’un, Masallatai da sauran wuraren Ibada, domin kuwa a cewar sa, a halin da ake ciki kasar Amurka na bukatar karin addu’o’i ne ba takaita su ba.

Zuwa wannan lokaci dai annobar coronavirus ta halaka mutane sama da dubu 94 a Amurka, daga cikin sama da miliyan 1 da suka kamu da cutar, abinda ya sanya ta zama kasa ta farko a duniya da annobar ta fi yiwa barna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.