Coronavirus-Duniya

A shirye muke mu bada damar sabon binciken kasa da kasa kan coronavirus - China

Wang Yi, Ministan harkokin wajen kasar China.  24/5/2020
Wang Yi, Ministan harkokin wajen kasar China. 24/5/2020 REUTERS / CHINA DAILY

China ta ce a shirye take ta baiwa tawagar kwararrun jami’ai na kasa da kasa damar gudanar da sabon bincike mai zaman kasa, kan asali kwayar cutar coronavirus da kuma yadda aka yi ta yadu.

Talla

Sai dai yayin sanar da matsayin na su, ministan harkokin wajen China Wang Yi, ya ce ya zama dole a kaucewa sanya siyasa cikin sabon binciken.

Wang Yi, ya kuma yi tur da abinda ya kira yunkurin gwamnatin shugaban Amurka Donald Trump na yada bayanan karya kan annobar coronavirus, domin bata sunan kasar China a idanun duniya.

A ‘yan makwannin da suka gabata, Amurka da Australia suka matsa wajen ganin an kafa tawagar masu bincike kan annobar da ta bulla a birnin Wuhan na China cikin watan Disambar bara.

Shugaban Amurka Donald Trump da Sakatarensa Mike Pompeo na cigaba da zargin China da kirkirar cutar daga wani dakin gwaje-gwajenta a Wuhan, da kuma boye bayanan da za su taimakawa kasashe da sauran hukumomin lafiya wajen dakile yaduwa da barnar annobar da kawo yanzu ta halaka sama da mutane dubu 340 a kusan kasashe 200.

Sai dai a nasu bangaren mafi akasarin kwararru a kimiyya sun yi amannar cewa kwayar cutar ta coronavirus ta samo asali ne daga dabbobi a wata kasuwar naman ruwa zuwa gad an adam.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.