Duniya-Coronavirus

Coronavirus: Sama mutane miliyan 2 sun warke, kusan dubu 345 sun mutu

Jami'an lafiya a Spain yayin tafawa mutanen dake yi musu jinjinar ban girma a birnin Madrid. 1/4/2020.
Jami'an lafiya a Spain yayin tafawa mutanen dake yi musu jinjinar ban girma a birnin Madrid. 1/4/2020. AP

Hukumomin lafiya sun ce yawan rayukan mutanen da annobar coronavirus ta halaka a sassan duniya ya kai dubu 343, 211, tun bayan bullarta daga daga kasar China a watan Disamban shekarar bara.

Talla

Akalla mutane miliyan 5 da dubu 362 da 160 suka kamu da cutar a tsakanin kasashe kusan 200, sai dai daga cikinsum, miliyan 2 da dubu 79 da 300 sun warke daga cutar.

Sabbin alkalumman sun kuma ce cikin awanni 24 da suka gabata, mutane dubu 3 da 441 annobar ta coronavirus ta kashe a fadin duniya, yayinda aka samu sabbin kamuwa da cutar dubu 99 da 827.

Har yanzu annobar ta fi muni a kasra Amurka, inda ta halaka jumillar mutane dubu 97 da 430, daga cikin miliyan 1 da 633 da 76 da suka kamu, yayinda wasu dubu 361 da 239 suka warke.

Sauran kasashen dake kan gaba wajen fuskantar kaifin annobar at COVID-19 sun hada da Birtaniya, inda cutar ta halaka mutane dubu 36 da 793, sai Italiya da ta rasa mutane dubu 32 da 785, Spain dubu 28 da 772, yayinda a Faransa annobar ta kashe mutane dubu 28 da 367.

A dunkule nahiyar Turai ta rasa jumillar mutane dubu 173 da 915 a dalilin annobar, yayinda Amurka da Canada suka rasa mutane dubu 103 da 889.

A nahiyar Kudancin Amurka da Caribbean coronavirus ta kashe mutane dubu 39 da 166, Asiya dubu 13 da 992, Gabas ta Tsakiya mutane dubu 8 da 805 sai kuma nahiyar Afrika inda cutar ta halaka mutane dubu 2 da 314 daga cikin dubu 109 da 562 da suka kamu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.