Isra'ila

Fira Ministan Isra'ila ya gurfana gaban kotu bisa tuhumar cin hanci

Fira Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu yayinda ya bayyana gaban kotu a birnin Kudus bisa tuhumar laifin cin hanci.
Fira Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu yayinda ya bayyana gaban kotu a birnin Kudus bisa tuhumar laifin cin hanci. Reuters

Fira Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya gurfana gaban wata kotun kasar dake birnin Kudus, domin fuskantar shara’a kan tuhume-tuhumen da ake masa na aikata laifukan karbar rashawa da cin amanar kasa.

Talla

Sai dai yayin zaman kotun, Netanyahu ya musanta dukkanin zarge-zargen da ake masa, wadanda ya bayyana a matsayin bita da kullin siyasa kawai domin bata masa suna da zummar ganin bayan gwamnatin da yake jagoranta.

Cikin watan Nuwamban shekarar bara, binciken masu gabatar da kara ya bayyana samun Fira Minista Netanyahu da laifin karbar kyautuka ba bisa ka’ida ba daga wasu attajirai, gami da kulla yarjejeniyar bayan fage da shugabannin wasu kafafen yada labarai domin su rika baiwa siyasarsa fifiko yayin gudanar da ayyukansu.

Karo na farko kenan a trihin Isra’ila da Fira Minista mai ci ke gurfana gaban shari’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.