WHO-Coronavirus

WHO ta dakatar da gwajin maganin Chloroquine kan masu cutar corona

Wani jami'in lafiya rike da maganin hydroxychloroquine, da a baya ake amfani da shi wajen kokarin warkar da masu cutar coronavirus.
Wani jami'in lafiya rike da maganin hydroxychloroquine, da a baya ake amfani da shi wajen kokarin warkar da masu cutar coronavirus. Yves Herman/Reuters

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bayyana dakatar nazarin da kwararru ke yi kan Hydroxy-chloriquine wajen gwajinsa a matsayin maganin cutar coronavirus.

Talla

Matakin na hukumar WHO ya biyo bayan rahoton masanan da fitacciyar mujallar kiwon lafiya ta Lancet ta wallafa a makon jiya, dake cewar amfani da maganin na Hydroxy-chloriquine kan masu cutar coronavirus na tsananta musababbin mutuwarsu ce, a maimakon warkewa.

Shugaban Hukumar Lafiyar ta Duniya, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce, dakatarwar ta wucen-gadi ce, yayinda daruruwan asibitoci daga sassan duniya ke amfani da maganin kan masu dauke da coronavirus da zummar gano ko yana aiki.

Alal hakika dai, ana amfani da hydroxy-chloroquine ne don magance kumburi da kuma daskarewar gabobin biladama, amma shugaban Amurka Donald Trump ya fito karara a makon jiya, inda ya bayyana wa duniya cewa, lallai yana kwankwadar wannan magani, a bin da ya sa a yanzu kasashen duniya ke ta rige-rigen sayen adadi mai yawa na maganin.

Shi ma Ministan Lafiyar Brazil, ya ce, hydroxy-chloroquine gami da maganin cutar Malaria, na magance cutar COVID-19, amma ga wadanda ba ta tsanata ba a jikinsu.

Sai dai a cewar Mujallar Lancet, magungunan guda biyu, za su iya haddasa wasu cutuka daban kamar rashin buguwar zuciya cikin tsanaki.

Mujallar ta kara da cewa, har ila yau, babu wani mutun dauke da cutar coronavirus da ke jinya a asibiti da ya ga alfanun wadannan magunguna guda biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.