Duniya-Coronavirus

Fitattun mutane na zargin Bill Gates da hannu wajen kirkirar cutar coronavirus

Hamshakin attajirin duniya Bill Gates, da ya mallaki fasahar na'ura mai kwakwalwa da Microsoft.
Hamshakin attajirin duniya Bill Gates, da ya mallaki fasahar na'ura mai kwakwalwa da Microsoft. REUTERS/Tiksa Negeri

A daidai lokacin da annobar coronavirus ke cigaba da yin ta’adi a duniya, ta fuskokin halaka rayuka da karya tattalin arzikin kasashen duniya, wani sabon lamari dake daukar hankali a yanzu, shi ne yadda wasu da dama, ciki harda fitattun mutane, musamman a nahiyar Afrika, ke alakanta annobar da hamshakin attajirin duniya wato Bill Gates.

Talla

A ranar 15 ga watan Maris da ya gabata, gwamnan Nairobi babban birnin Kenya Mike Sanko, ya wallafa wani tsohon bidiyon attajirin duniya Bill Gates na shekaru 5 da suka gabata, da a cikinsa yake gargadin cewa duniya ka iya fuskantar bala’in annoba iri-iri a shekarun dake tafe.

A waccan lokacin, duk da cewa Bill Gates bai ambaci sunan coronavirus ba, Gwamna Sanko na Kenya ya baiwa bidiyon sunan ‘Gates ya bamu labarin barkewar annobar Corona’.

Tuni dai mutane sama da miliyan 1 suka yada wanna bidiyo, yayinda wasu mutanen kusan miliyan 38 suka kalli bidiyon na Bill Gates ta kafafen sadarwa na zamani, abinda ya kara karfin zargi ko jita-jitar da ake yadawa ta cewar hamshakin attajirin na da hannu a wajen kirkirar cutar. Kafin wallafar da gwamnan Nairobi yayi, a baya an yada makamancin wannan zargi a shafukan Internet wanda aka yi musayarsa tsakanin mutane masu yawan gaske aka kuma kalla sau sama da miliyan 53.

Bayaga ‘yan siyasar Kenya, a Najeriya ma akwai masu wannan ra’ayi na alakanta hamshakin attajirin duniyar da annobar coronavirus, inda a kwanakin baya tsohon ministan sufurin jiragen sama a kasar Femi Fani Kayode, ya yada wannan zargi ta kafofin sadarwa na zamani, inda yace Bill Gates na cikin gungun hamshakan duniyar dake son mulkar dan adam ta hanyar amfani da annobar cutuka da kuma fasahar 5G, wadda har yanzu ake dambarwa akanta tsakanin Amurka da China.

Masu wannan ra’ayi dai musamman a nahiyar Afrika, na zargin cewa Bill Gates na son mulkar duniya ne ta hanyar amfani da kimiyya da kuma kokarin habaka arzikinsa ta hanyar samar da rigakafin cutar coronavirus, wanda tuni gidauniyarsa ta Bill and Melinda Gates ta mallaka shekaru da dama da suka gabata kafin su kirkiri cutar.

Bill Gates na fuskantar wannan tuhuma ta hannu wajen kirkira da kuma yada annobar coronavirus ce, duk da irin makudan kudaden da yake narkawa a kasashe maso tasowa musamman a Afrika, wajen tallafawa lafiya, ilimi da kuma habaka tattalin arziki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.