Duniya

Mutane kusan dubu 100 coronavirus ta halaka a Amurka kadai

Jami'an lafiyar Amurka yayin daukar wani mai dauke da cutar coronavirus a yankin Shawnee, dake jihar Oklahoma.  2/4/2020.
Jami'an lafiyar Amurka yayin daukar wani mai dauke da cutar coronavirus a yankin Shawnee, dake jihar Oklahoma. 2/4/2020. REUTERS/Nick Oxford

Bayan shafe akalla watanni 5 da bullarta daga China a karshen shekarar bara zuwa yau, annobar COVID-19 ta halaka sama da mutane dubu 352 a kasashe kusan 200.

Talla

Yanzu haka a Amurka kawai annobar ta halaka mutun kusan dubu 100.

Alkalumma hukumomin lafiya na kasa da kasa da kamfanin dillancin labarai na AFP ke tattatarawa sun nuna cewar zuwa daren jiya, mutum dubu 352 da 494 wannan annoba ta halaka a fadin duniya, daga cikin mutane miliyan 5 da dubu 638 da 190 da suka kamu, yayinda akalla miliyan 2 da dubu 236 da 200 suka warke.

Kasashen da annobar ta fi yi wa ta’adi a duniya sun hada da Amurka, inda a nan kawai mutane dubu 99 da 724 cutar ta halaka, a Birtaniya kuma mutane dubu 37 da 460, sai Italiya da ta rasa mutane dubu 33 da 072, a Faransa rayuka dubu 28 da 596 cutar ta lakume, yayinda a Spain ta halaka mutane dubu 27 da 118 suka mutu.

A Brazil kasar da annobar ta COVID-19 ta fi yiwa ta’adi a nahiyar Kudancin Amurka, jumillar mutane dubu 25 da 598 suka mutu, bayan mutuwar karin mutane dubu 1 da 86 cikin sa’o’i 24 da suka gabata, sai Afrika, inda cutar ta kashe mutane dubu 3, 637 daga cikin dubu mutane dubu 121 da 522 da suka kamu, sama da dubu 47 kuma suka warke.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI