Kimiya

An sauya ranar tashin 'yan sama jannati daga Amurka zuwa duniyar wata

Kumbon Falcon 9 mallakin cibiyar SPACE X da aka dakatar da tashinsa dauke da 'yan sama jannati 2 zuwa duniyar wata, saboda rashin kyawun yanayi.
Kumbon Falcon 9 mallakin cibiyar SPACE X da aka dakatar da tashinsa dauke da 'yan sama jannati 2 zuwa duniyar wata, saboda rashin kyawun yanayi. JOE RAEDLE / GETTY IMAGES NORTH AMERICA / GETTY IMAGES VIA AFP

An jingine tafiya duniyar sama da wasu ‘yan sama jannati biyu na Amurka suka shirya yi da safiyar ranar Laraba, wanda shekaru masu yawa kasashen duniya ke wannan sai da rai.

Talla

Jingine tafiya sararin samaniyar da aka yi dai na biyo bayan rashin kyawun yanayi, inda aka sami mahaukaciyar iska da goguwa a kudancin Carolina, wanda aka gano cewa akwai hadarin gaske idan ‘yan sama jannatin suka tashi.

Cibiyar Binciken sararin samaniya ta NASA da Jami’an wannan sabon yunkuri na tafiya duniyar sama, da ake kira SPACE X a yanzu saun tsayar da asabar mai zuwa a matsayin ranar cika burin na tafiya zuwa duniyar wata.

Shugaban cibiyar SPACE X Elon Musk ya ce tun kafa cibiyar a shekara ta 2002 suke ta fatan samun wannan dama don tafiya duniyar wata.

Ana sa ran ‘yan sama jannatin biyu su tashi ne daga cibiyar binciken yanayi ta Kennedy, inda nan ne shahararren dan sama jannatin nan Neil Armstrong da ayarinsa na kumbo appolo 11 suka tashi zuwa duniyar wata a shekarun baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.